Da yake karin haske game da ikirarin hukumar ta tsaro, shugaban ta Alexander Bortnikov, ya shaidawa taron manyan jami'an kasar wanda shugaba Vladimir Putin ya jagoranta, cewa kwararru sun tabbatar da wani bam mai karfin gaske ne ya fashe a cikin jirgin, wanda hakan ne kuma ya sanya jirgin tarwatsewa.
Bisa wannan sakamako, shugaban kasar ta Rasha Vladimir Putin, ya umarci sassan hukumomin tsaron kasar sa, da su gaggauta damke dukkanin wadanda ke da hannu a aikata wannan ta'asa a duk inda suke a fadin duniya.
Tuni dai FSB ta bayyana tukwicin dalar Amurka miliyan 50, ga duk wanda ya bada muhimman bayanai da za su taimaka, wajen cafke masu hannu cikin kitsa faduwar jirgin fasinjar kasar ta Rasha.