in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rasha ta dakatar da samar da iskar gas ga Ukraine
2015-11-26 10:54:19 cri
Kamfanin Gazprom na kasar Rasha ya sanar a jiya Laraba 25 ga wata cewa, za a dakatar da samar da iskar gas ga kasar Ukraine.

Shugaban kamfanin Gazprom Alexei Miller ya bayyana wa 'yan jarida a wannan rana cewa, ya zuwa karfe 10 na safiyar ranar nan, Ukraine ta riga ta samu dukkan iskar gas da ta saya da kudin ta, don haka kamfanin Gazprom ba zai samar da iskar gas ga kasar Ukraine ba kafin Ukraine ta sake biyan wani kudin don kara sayen iskar gas daga kamfanin.

Bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na ITAR-TASS ya bayar, an ce, gwamnatin kasar Ukraine ta zartas da kudurin a wannan rana cewa, ta umurci kamfanin man fetur da iskar gas na kasar ta da ya dakatar da ci gaba da sayen iskar gas daga kasar Rasha.

Firaministan kasar Ukraine Arseni Jazenjuk ya bayyana cewa, an tsaida kudurin domin farashin iskar gas da sauran kasashen Turai suke sayar ma kasar Ukraine ya fi araha. Kana yawan iskar gas da kasar Ukraine ta ke amfani da shi ya ragu da kashi 20 cikin dari.

A wannan rana, firaminsitan kasar Ukraine Arseni Jazenjuk ya sanar a majalissar zartarwar kasar cewa, gwamnatin ta tsaida kudurin rufe yankin sama na kasar ga kamfanin jiragen sama na kasar Rasha. Ma'aikatar ayyukan more rayuwa ta kasar Ukraine ta sanar da cewa, za a fara aiwatar da kudurin tun daga ranar 26 ga wata. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China