in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ba a gano dalilin faduwar jirgin saman Rasha ba
2015-11-08 13:54:39 cri
Kwamitin binciken dalilin faduwar jirgin saman kasar Rasha dake karkashin jagorancin kasar Masar, ya bayyana a ran 7 ga wata cewa, za a ci gaba da yin nazari kan akwatunan nadar bayanai na jirgin sama, dalilin hake ne har yanzu ba a da tabbaci kan dalilin da ya haddasa faduwar jirgin saman din ba.

Haka kuma, dangane da bayanan da wasu kafofin watsa labaran yammacin kasashe suka bayar, an ce, 'yan ta'adda suka sa boma-bomai cikin jirgin saman din, lamarin da ya janyo faduwar jirgin, shugaban kwamitin bincike, Ayman al-Mokadem ya bayyana cewa, babu wata shaidar dake tabbatar da hakan, haka kuma, ya nuna fatan kafofin watsa labarai da suka fitar da irin wadannan bayanai za su iya taimaka wa kwamitin wajen gudanar da bincike. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China