in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka ta ce ba ta da alaka da harbo jirgin saman yaki na Rasha
2015-11-25 14:15:28 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amurka Steven Warren a jiya talata ya ce, batun harbon jirgin saman yakin Rasha tsakanin kasashen Rasha da Turkiya ne kawai, Amurka ba ta da hannu a ciki.

A gun taron manema labaru da aka yi a wannan rana, Mr. Warren ya ce, harbo jirgin saman yakin Rasha da Turkiya ta yi abu ne da ya shafi gwamnatocin kasashen Turkiya da Rasha da sojojinsu kawai, domin yayin da lamarin ya auku, jirgin saman yakin kasar Amurka samfurin F-15C da yake taimakawa Turkiya don sintiri ba ya kusa da wurin.

Mr. Warren ya ce, wurin da lamarin ya auku, yankin tsaunuka ne, kuma bangarorin biyu sun yi taho-mu-gama ne a sararin samaniyya, saboda haka akwai wuya, a tabbatar da cewa, ko jirgin saman yakin Rasha ya tsallake iyakar kasashen Turkiya da Siriya. Amma, abu daya da aka iya tabbatarwa, shi ne, lamarin nan ya auku a kan iyakar kasashen Turkiyya da Siriya.

Warren ya ce, Amurka ta sa ido tare da gano cewa, sojojin Turkiyya sun yi kashedi ga jirgin saman yakin Rasha, amma matukin jirgin na Rasha ya yi shiru, bai fadi kome ba.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China