Shugaban kasar Sin Xi Jinping zai kai ziyarar aiki kasar Zimbabwe, tun daga ran 1 zuwa na 2 ga watan Disambar dake tafe, wannan ziyarar za ta kasance ta farko da shugaban kasar Sin zai gudanar a Zimbabawe, tun bayan shekaru 20 da suka gabata.
Game da hakan, shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe ya nuna kyakkyawan fata ga ziyarar ta shugaba Xi a wannan karo. Mugabe ya kuma ce hakan zai ba su damar tattaunawa kan wasu ayyuka, da shirye-shirye, kana Zimbabwe na fatan Sin a matsayin sahihiyar kawarta, za ta gabatar da taimako gare ta. Ya ce ziyarar Mista Xi a wannan karo za ta zamo babban ci gaba tsakanin kasashen biyu.
Ban da wannan kuma, game da taron koli na dandalin tattaunawar hadin kai tsakanin Sin da Afrika da za a kira a Afirka ta kudu, a ganin Mista Mugabe, taron zai sa kaimi ga bunkasuwar dangantakar dake tsakanin Sin da Afrika. A cewarsa, dandalin ya riga ya sa kaimi ga mu'ammala tsakanin Sin da Afrika ta kudu, wanda hakan ya zamo wata babbar nasara ga kasashen. Shugaba Mugabe ya kara da cewa zai halarci taron a matsayin sa na shugaban kasar dake rike da shugabancin kungiyar AU. (Amina)