in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Mugabe na Zimbabwe ya bukaci inganta kwarewar masana'anru lu'u lu'u
2014-11-07 16:52:58 cri
Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mogabe a ranar Alhamis din nan ya yi kira da a kara zuba jari a fasaha domin kasar ta amfana daga lu'u lu'unta.

Mugabe ya ce rashin fasaha ya kawo cikas a Zimbabwe da aka kiyasta yana da dimbin lu'u lu'u da zai isa gamsar da kashi 25 a cikin 100 na kasuwannin duniya.

Da yake jawabi a wajen bude taro akan lu'u lu'u a Babban birnin kasar , yace wannan albarkatu ya kamata a yi takara kan shi a yankin da sauran kasuwannin kasashen duniya. Don haka yake kalubalantar masana dasu samar da hanyoyi na fito da fasahar wadanda ke nan yanzu da wanda zasu taso nan gaba da aka samo daga bincike da fasaha don ganin an bayyana darajar su. Tun lokacin da ta fara sai da lu'u lu'u a kasuwannin duniya a shekara ta 2009, Zimbabwe ta dago zuwa matsayi na 6 a duniya wajen sai da lu'u lu'u, ganin ta samar da kashi 8 a cikin 100 a duniya a shekara ta 2012 lokacin da adadin karatin da aka samu a wannan lokacin baki daya ya tsaya a miliyan 12.(Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China