in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zimbabwe na ci gaba da fitar da lu'u lu'u, in ji ministan ma'adanan kasar
2014-08-05 10:13:50 cri

Ministan ma'adanai na kasar Zimbabwe Walter Chidhakwa, ya ce har yanzu ana ci gaba da haka tare da fitar da danyen lu'u lu'u a kasar, kasancewar ikon sarrafa shi a gida bai taka kara ya karya ba.

Mr. Chidhakwa wanda ya bayyana hakan ga kwamitin makamashi na majalissar dokokin kasar a jiya Litinin, ya ce za a ci gaba da kara yawan danyen lu'u lu'u da ake sarrafawa a cikin kasar sannu a hankali, ya zuwa lokacin da za a kai ga iya sarrafa isasshen lu'u lu'un a gida.

Kasar Zimbabwe dai ta fara aikin hakar duwatsu masu daraja a gabashin kasar tun cikin shekara 2009. Kuma ya zuwa yanzu ta fitar da nau'o'in irin wadannan duwatsu masu daraja na miliyoyin daloli.

Game da sauran nau'o'in duwatsu masu daraja da kasar ke hakowa kuwa, Mr. Chidhakwa ya ce, gwamnatin na kokarin tantance yawan Platinum da ake haka a kasar, tare da fatan kafa masana'antar sarrafa shi. Ana dai amfani da wannan nau'i na dutse mai daraja ne wajen kirar zinari, da Azurfa da dai sauransu.

A daya bangaren kuma, ministan na ma'adanai ya ce, a halin da ake ciki, kasuwar zinarin kasar na farfadowa bayan dan koma-baya da ta samu tsakanin shekaru 10 da suka gabata. Ya ce, a bara kadai kasar ta fidda kilogiram 14,065 na zinari, wanda darajarsa ta kai dala miliyan 626.11, adadin da ya gaza kilogiram 14,472 da ta fitar a shekarar 2012. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China