Shugaba Mugabe ya ce, dangantaka tsakanin kasashen biyu na da dogon tarihi. Yayin da jama'ar Zimbabwe suke gwagwarmaya domin samun 'yancin kai, Sin ta ba da gudummawa sosai. 'Ba za a manta da wannan taimako ba, kuma ba za a manta cewa jama'ar Sin aminanmu ne ba a duniya', a cewar shugaban..
Yayin da jama'ar Zimbabwe suke gwagwarmaya wajen yaki da 'yan mulkin mallaka bisa jagorancinsa a shekarar 1977, Robert Mugabe ya taba kawo ziyara a Sin. Tun bayan da ya dauki mulkin kasarsa, ya taba kawo ziyara a Sin sama da sau 10, har ma ya kasance daya daga cikin shugabannin kasashen Afirka da suka fi kawo ziyara a kasar Sin. A sabili da haka, an rada masa suna 'abokin Sinawa da aka fi samun fahimta'. (Fatima)