in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sinawa dake Zimbabwe sun taya yara marayun kasar murnar ranar yara
2015-06-01 10:20:01 cri
A jiya Lahadi 31 ga watan Mayu ne kungiyar 'yan kasuwa Sinawa dake Zimbabwe, da hadin gwiwar sauran kungiyoyin Sinawa mazauna kasar, suka gudanar da bikin taya yara marayu 400 na Zimbabwe murnar ranar yara, a unguwar da Sinnwa ke zaune dake birnin Harare.

Kungiyar masu aikin jin kai dake kasar Zimbabwe ta bayyana cewa, akwai marayu kimanin miliyan 1 da dubu 300 a kasar, adadin da ya kai kashi daya cikin goma na daukacin al'ummar kasar. Kana cikin adadin jimillar marayun, kashi 40 cikin dari yara ne dake kasa da shekaru 15, wadanda yawancinsu ba sa samun isassun kayayyakin more rayuwa.

Yayin wannan biki, masu aikin sa kan na kasar Sin fiye da su 50, da takwarorin su 'yan kasar ta Zimbabwe sun bayar da abinci, da kayayyakin rubutu, da jakar littafi ga yaran. Kana kwalejin Confucius dake jami'ar Zimbabwe ta kafa wani dandali mai alamta al'adun kasar Sin, domin yin bayani ga yaran don gane da al'adun kasar Sin.

Babbar sakantariyar kungiyar 'yan kasuwa Sinawa a kasar Li Manjuan, ta bayyana cewa, makasudin gudanar da bikin shi ne, baiwa yara marayun kasar ta Zimbabwe damar kara samun tallafi, tare da fayyace musu al'adun kasar Sin, da kara sa kaimi ga mu'amala, da fahimtar juna a tsakanin al'ummun kasashen Sin da na Zimbabwe. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China