Wanni jami'in hukumar kasar ya bayyana wa majiyarmu cewa, an tattake mutane da dama, yayin da kimanin mutane 30,000 ke kokarin fita daga filin wasan da aka gudanar da taron a ranar Alhamis, a garin Kwekwe mai nisan kilomita 213 daga birnin Harare.
Jami'in gwamnatin kasar mai suna Shadreck Mubaiwa, ya ce yamutsin ya auku ne sakamakon kankantar filin wasan, wanda ke da kofa daya tak, kuma bisa tsarin gininsa yana iya daukar mutane 7000 ne kawai. Bugu da kari Mubaiwa ya musanta zargin da ake yi cewa 'yan sanda ne suka haddasa lamarin, sakamakon barkonon tsuhuwa da aka ce sun jefa cikin dandazon jama'ar da suka halarci addu'o'in.
Wani malamin coci mai suna Walter Magaya ne dai ya jagoranci taron, mutumin da ya kasance daya daga mafiya janyo cincirindon jama'a, yayin tarukan addu'o'i a kasar. (Saminu Alhassan)