Shugaban Zimbabwe ya yi kira da a tabbatar da sakamakon da aka samu a taron shugabannin kasashen Asiya da na Afirka
A yau Jumma'a 24 ga wata, shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe ya halarci bikin tunawa da ranar cika shekaru 60 da kiran taron Bandung, inda ya yi kira da cewa, kamata ya yi kasashen Asiya da na Afirka su karfafa hadin gwiwa domin tabbatar da sakamakon da aka samu a taron shugabannin kasashen Asiya da na Afirka yadda ya kamata, a kokarin canza yanayin da kasashe masu tasowa ke ciki na rashin samun adalci a fannonin siyasa da tattalin arziki da cinikayya na duniya a cikin 'yan shekaru sama da 10 da suka wuce.
A cikin jawabinsa, shugaba Mugabe ya ce, a cikin 'yan shekarun da suka wuce, kasashe masu tasowa na kokarin neman wani tsari tsakanin bangarori da dama, amma ba tare da samun matsayi a cikin tsarin na kungiyoyin duniya ba. A yanzu kuma lokacin ya yi na sake yin amfani da ra'ayin Bandung domin canza yanayin da ake ciki.(Fatima)