A yayin ganawar, Fan Changlong ya ce, tun bayan da aka kulla huldar diplomasiya tsakanin Sin da Zimbabwe, dangantakar dake tsakanin kasashen biyu na samun ci gaba yadda ya kamata, kuma manyan jami'ai na kara kai wa juna ziyara. Ya kara da cewa, kasar Sin na mayar da hankali sosai kan hadin kai a dukkan fannoni tsakanin rundunonin sojojin kasashen biyu.
A nasa bangaren, Sydney Sekeramayi ya bayyana cewa, ana ta gudanar da hadin kai mai inganci tsakanin kasashen biyu ta fuskar aikin tsaro, don haka ya yi fatan za a karfafa yin cudanya da hadin kai tsakanin rundunonin sojojin kasashen biyu a nan gaba. (Bilkisu)