Jakadan Sin a kasar Zimbabwe Lin Lin ya bayyana a cikin jawabinsa cewa, kasar Sin za ta ci gaba da bude kofa ga kasashen ketare da yin kwaskwarima a gida, da bunkasa kasa cikin lumana, kana za ta kara bayyana ra'ayoyin kasashe masu tasowa da kuma taimake su wajen neman moriyar kansu a harkokin duniya. Jakadan kuma ya jaddada cewa, kasar Sin ta dora muhimmanci sosai kan dangantakar dake tsakaninta da kasashen Afirka, an samu nasarori da kyakkyawan sakamako kan ziyarar shugaban kasar Sin Xi Jinping a kasashen Afirka a bara, bisa wannan tushe Sin za ta kara yin hadin gwiwa a tsakanin sassan biyu a dukkan fannoni bisa ka'idojin nuna gaskiya na hakika, da sada zumunta.
A daya hannun kuma jakadan ya bayyana cewar bayan da cutar Ebola ta bullo, kasar Sin ta tura masu aikin jinya zuwa kasashe masu fama da cutar nan take don taimaka masu wajen yaki da cutar, abin da ya bayyana kyakkyawar zumunta a tsakanin Sin da kasashen Afirka. (Zainab)