Yayin rantsuwar da ya yi, mataimakin shugaban kasar na farko, Emmerson Mnangagwa ya bayyana cewa, har abada zai sadaukar da ransa ga kasar Zimbabwe.
Sauran wadanda aka rantsar sun hada da mataimakin shugaban kasar na biyu, Phelekezela Mphoko, da ministan matasa, da na harkokin tattalin arziki, da na bunkasa makamashi da wutar lantarki, da ministan tarbiya a matsayin koli, da dai sauran su.
Manyan jami'an gwamnatin dai sun maye gurbin wadanda guguwar sauyi ta yi awon gaba da mukaman su ne cikin 'yan kwanakin baya.
Emmerson Mnangagwa mai shekaru 68 a duniya, muhimmin mashawarci ne ga shugaba Mugabe, ya kuma taba rike matsayin ministan tsaron kasar, da ma wasu manyan mukamai. Kafin nadin sa shi ne ministan shari'ar kasar tun daga watan Satumbar bara. An kuma zabe shi a matsayin wanda zai maye gurbin tsohuwar mataimakiyar shugaban kasar Joyce Mujuru, wadanda da aka yi zaton sun fi kowa dacewa su maye gurbin shugaba Mugabe.
A ranar 9 ga watan nan ne dai shugaba Mugabe ya sanar da korar tsohuwar mataimakiyarsa Joyce Mujuru, da sauran membobin majalisar ministocinsa su 7. Kafin hakan shugaba Mugabe, ya taba zargin Mujuru, da magoya bayanta, da laifin yunkurin hallaka shi, koda yake dai Mujuru ta musunta hakan. (Fatima)