in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Zimbabwe ya jinjinawa zumuncin dake tsakanin kasarsa da Sin
2014-08-24 20:17:11 cri
Yanzu haka shirye shirye sun yi nisa game da ziyarar aiki da shugaba Robert Mugabe na Zimbabwe zai kawo nan kasar Sin, tun daga ranar 24 zuwa 28 na wannan wata da muke ciki.

Tun ma kafin fara ziyarar tasa bisa gayyatar da shugaban kasar ta Sin Xi Jinping ya yi masa, shugaba Mugabe ya bayyana wa kafofin watsa labaran kasar Sin cewa, dangantakar sada zumunta tsakanin Zimbabwe da kasar Sin na da dadadden tarihi, irin wanda ake fatan dorewarsa cikin kyakkyawan yanayi.

Mr. Mugabe ya ci gaba da cewa, karkashin zumuntar dake tsakanin sassan biyu, kasar Sin ta ba da goyon baya da taimako matuka ga jama'ar kasarsa, tun lokacin neman 'yancin kai, kuma jama'arsa ba za su manta da taimakon da kasar Sin ta gabatar musu ba.

Ya ce kasar Sin abokiyar arziki ce ga Zimbabwe a fannonin da suka shafi al'amuran kasa da kasa, wanda hakan ya sa jama'ar Zimbabwe daukar jama'ar kasar Sin tamkar 'yan uwa.

Bugu da kari, shugaba Mugabe ya ce kamata ya yi Zimbabwe da kasar Sin su ci gaba da karfafa hadin gwiwarsu, da taimakon junansu bisa burin neman bunkasuwar tattalin arziki, wanda hakan ne ma ya sa yayin ziyararsa a nan kasar Sin, zai tattauna da wasu wakilan kasar Sin kan hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya dake tsakanin kasashen biyu, da fatan hakan zai bada damar inganta hadin gwiwar kasashen biyu, musamman ma a fannonin gine-ginen ababen more rayuwa, da sarrafa hajojin noma da ma'adinai. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China