in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta tallafawa kasarZimbabweda shinkafa
2015-03-17 14:59:50 cri
Gwamnatin kasar Sin ta tallafawa kasar Zimbabwe da shinkafa wadda yawanta ya kai Tan 5400, a wani mataki na taimakawa kasar wajen warware matsalar karancin abinci.

Yayin bikin mika wannan kyauta da aka gudanar ranar Litinin a birnin Harare hedkwatar kasar Zimbabwe, minista mai kula daharkokin kwadago da zamantakewar al'ummarkasarZimbabwe Prisca Mupfumira, ta jinjina gudummawar da Sin ke baiwa kasar ta Zimbabwe, musamman a lokacin dakasar ke cikin mawuyacin hali.

Mupfumira ta ce, za a mika shinkafar ga al'ummar kasar mafiya bukata, matakin da ta ce zai taka muhimmiyar rawa wajen warware matsalar karancin abinci da kasar ke fuskanta cikin 'yan shekarun nan.

Minista Prisca ta kara da cewa, marasa galihu na fuskantar matsalar karancin abinci, sabo da haka ya kamata gwamanatin ta dubi halin da suke ciki, musamman ma tsofaffi da kananan yara, da nakasassu, da iyalan dake cikin kangin talauci, da mutanen da aka tsare a gidan yari.

Da yake nasa jawabi, mukaddashin jakadan kasar Sin a kasar ta Zimbabwe Cui Chun, ya ce a matsayin babbar abokiyar kasar Zimbabwe, Sin ta fahimci muhimmancin aikin gona a kasar Zimbabwe, kuma tana da niyyar taimakawa kasar wajen raya wannan fanni, da kyautata ingancinsa,don tabbatar da samar da isasshen abinci ga al'ummar kasar baki daya.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China