A cikin watan Janairu, gwamnatin Zimbabwe ya tilasta biyan haraji ga otel otel din kasar dake karbar masu yawon shakatawa daga kasashen waje, lamarin da ya gurguntar da ci gaban bangaren yawo bude ido sosai.
Karbar wannan haraji ya maida kasar Zimbabwe yankin mafi tsada a fannin yawon shakatawa a lokacin da kasar ke bukatar janyo hankalin masu yawon bude ido wanda kuma yawansu ya ragu sosai a tsawon shekaru goma na baya bayan nan, in ji masu ruwa da tsaki a fannin harkokin yawon bude ido. A lokacin baya, ba a biya haraji kan wurin kwana da sauran ayyuka ga masu yawon bude ido daga kasashen waje. (Maman Ada)