in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jiragen saman yakin kasar Faransa sun sake kai farmaki kan mayakan IS dake Iraqi
2015-11-25 10:49:07 cri

Kafar yada labaru ta kasar Faransa ta ruwaito wani jami'in kasar na cewa, wani jirgin saman yakin kasar Faransa ya tashi daga babban jirgin ruwan yaki mai saukar jiragen sama mai taken Charles De Gaulle zuwa kasar Iraqi, inda ya yi luguden wuta kan sansanonin mayakan IS dake kasar.

Sanarwar ta ce, farmakin da aka kai na wannan karo ya lalata wata cibiyar ba da umurni dake birnin Tal Afarna na Iraqin. Har wa yau hedkwatar rundunar soja ta kasar Faransa ta ba da labari a ran 24 ga wata cewa, Faransa ta aiwatar da wannan aiki ne da hadin gwiwar sojin Amurka.

A wani ci gaban kuma wasu rahotanni sun ce jirgin saman yaki dake tashi daga babban jirgin ruwan yaki mai saukar jiragen sama na Charles De Gaulle, ya kai farmaki kan wasu gine-ginen IS dake Iraqi a ranar Litinin, kuma a wannan rana jirgin saman yaki kirar "Dassault Mirage" ya tashi daga kasar Jordan, da wasu jiragen saman yakin kirar "Rafale combat" suka kuma kai farmaki kan sansanonin kungiyar ta IS dake kasar Sham. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China