Philip Hammond ya bayyana cewa, sakamakon shigowar Rasha, yanayin da ake ciki a Syria zai kara tsananta. A ganinsa, kamata ya yi kasashen Birtaniya da Amurka su yi shawarwari kan matsalar jin kai da batun 'yan gudun hijira na Syria da yaki da kungiyar IS da sauransu.
A nasa bangare, John Kerry ya furta cewa, ministocin tsaro na kasashen Amurka da Rasha sun riga sun yi musayar ra'ayi ta wayar tarho kan batun yaki da kungiyar IS, kuma Kerry ya kara da cewa, Amurka ta yi maraba da shigar kasar Rasha cikin wannan aiki. A sa'i daya, Kerry ya ce, Amurka a shirye take wajen yin shawarwari kan batun Syria, sai dai abin zai dogara ga ko shugaban Syria, Bashar al-Assad, da Rasha da suke da niyyar yin shawarwari.
Kafin wannan, Amurka ta rika bukatar ganin Bashar al-Assad da ya sauka daga mukaminsa na shugaban Syria. Amma a ranar 16 ga wata, Kerry ya nanata cewa, za a shafe dogon lokaci domin kammala wannan aiki. Kamata ya yi bangarori daban daban su cimma matsaya kan samun sakamako mai kyau.(Fatima)