A wannan rana, mujallar Dabiq karkashin shugabancin kungiyar IS ta wallafa hotuna kan yadda kungiyar ta harbe kawunan wadannan mutane biyu da bindiga, har suka mutu, amma kungiyar ba ta fayyace sunayen mutanen biyu ba.
Tun da farko dai kungiyar IS ta yi shelar cewa, tana garkuwa da wani Basine dan asalin birnin Beijing mai sunan Fan Jinghui da wani dan kasar Norway mai suna Ole Johan Grimsgaard-Ofstad.
A yau ne, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hong Lei ya ce, Sin ta lura da wadannan labaru, wadanda suka girgiza ta matuka, za ta ci gaba da tabbatar da sahihancin wadannan bayanai
A cewar kakakin, tun bayan da aka yi garkuwa da Basinen, gwamnatin Sin ke iyakacin kokarin ganin an ceton shi.(Bako)