Kwamitin sulhu ya kalubalanci kasashe membobin MDD masu karfi da su dauki kowane irin matakai a wuraren na Syria da Iraki dake hannun kungiyar IS, su yi hadin gwiwa domin yin rigakafi da yaki da kungiyoyin ta'addanci, kamarsu kungiyar IS, da ta Al-Qaeda da sauransu, domin rushe sansanoninsu a wadannan kasashen biyu.
A jiya kuma ma'aikatar harkokin waje ta Rasha ta ba da sanarwar cewa, ministan harkokin waje na Rasha Sergei Viktorovich Lavrov ya buga waya da sakataren harkokin waje na Amurka John Kerry a wannan rana, inda suka yi shawarwari kan yadda za su shawo kan matsalar kungiyar IS, da sa kaimi ga gwamnatin Syria da ta yi shawarwari da jam'iyyun adawa da gwamnati da sauransu. Ban da haka, bangarorin biyu sun yi shawarwari kan yadda za a tabbatar da sakamakon da aka samu a gun taron ministocin harkokin waje kan batun Syria a Vienna sau biyu. (Fatima)