in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rundunar tsaron Rasha ta hallaka 'yan ta'addan kungiyar IS su 8
2015-08-03 11:12:42 cri
Wata kafar yada labaru ta kasar Rasha ta ce hukumar yaki da ta'addanci ta kasar ta tabbatar da hallaka 'ya ta'adda 8 dake yankin Ingush kasar na Rasha

Kafar ta ce hukumar ta shaida cewa rundunar tsaron Rasha ta samu wannan nasara ne a jiya Lahadi. Ta ce wadannan mutanen sun shiga kungiyar IS a kwanan baya, kuma suna aikata laifuka masu alaka da ta'addanci, ciki hadda kashe ma'aikatan gwamnati, da neman kudi daga masana'antu ta barauniyar hanya. Rundunar tsaron kasar ta lura da tafiye-tafiyen su, ta hanyar sa ido kafin su kai ga kai musu hari.

Bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na TASS na Rasha ya bayar, an ce, bayan da aka yi kwarya-kwaryar bincike, an gano cewa a cikin 'yan ta'addan da aka kashe, har da wanda ya kulla makircin kai hare-hare ga gwamnatin Groznyy dake kasar ta Rasha a shekarar 2014.

Yanzu haka dai Rasha na fuskantar babban matsin lamba a fannin yaki da ta'addanci. Kaza lika hukumar tsaron kasar ta ce a yanzu haka 'yan ta'adda na yunkurin shiga kasar ta kan iyakokin kasashe da dama. (Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China