A wannan rana, a birnin Wanshington na kasar Amurka, Brennan ya ce, lamarin da ya auku a birnin Paris ya nuna cewa, kungiyar IS ta yi nisa wajen kulla makirci, kuma ta cimma nasarorin gudanar da wasu ayyukan ta'addanci.
A kwanakin baya ma, kungiyar ta kai hare-haren ta'addanci da dama a wasu kasashen duniya, ciki har da harin kunar bakin wake da aka dasa cikin wani ginin da ke kudancin birnin Beirut hedkwatar kasar Lebanon da kuma harin ta'addanci da aka kai a birnin Paris. Duk da cewa ana ci gaba da binciken musabbabin faduwar jirgin saman fasinja na kasar Rasha a yankin Sinai na kasar Masar, amma wani reshen kungiyar IS ya sanar da daukar alhakin hadarin jirgin. (Bako)