in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin sama na kasar Iraki sun kashe wasu madugan kungiyar IS
2015-08-31 14:01:03 cri
Rundunar sojan kasar Iraki ta sanar a ranar 30 ga wata cewa, sojojin saman kasar sun kai hari ta sama kan wani sansanin kungiyar IS dake jihar Anbar a yammacin kasar, wanda ya haddasa mutuwar wasu madugan kungiyar IS wadanda ake zargi da kaiwa wasu hafsoshin sojojin kasar biyu hari a kwanakin baya.

Hukumar hadin gwiwa ta bada umurni ta sojojin kasar Iraki ta bayar da sanarwa a wannan rana cewa, jiragen saman yaki na sojojin kasar Iraki sun kai hari ga wani gini na birnin al-Qaim da ke iyakar Iraki da Syria da ke hannun dakarun kungiyar IS, harin da ya haddasa mutuwar wasu dakarun kungiyar IS dake cikin ginin, ciki har da madugan kungiyar 5 wadanda suka tsara shirin kai hari ga manyan hafsoshi 2 na sojojin kasar Iraki a ranar 27 ga wata. Amma sanarwar ba ta bayyana hakikanin lokacin da aka kai harin ba.

Sanarwar ta bayyana cewa, bayan da hafsoshin biyu suka mutu a sakamakon harin, hukumar leken asiri da hukumar hadin gwiwa ta bada umurni ta sojojin kasar sun kaddamar da bincike don zakulo dakarun kungiyar IS da suka tsara shirin kai harin. A karshe an gano cewa sun buya ne a wani wuri a birnin al-Qaim dake da nisan kilomita kimanin 330 arewa maso yammacin birnin Baghdad . (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China