Kasashen Faransa da Amurka da Rasha za su tattauna hadin gwiwar yaki da kungiyar IS
Firaministan kasar Faransa Manuel Valls ya bayyana a ranar 17 ga watan nan cewa a mako mai zuwa, shugaban Faransa François Hollande zai gana da takwaransa na kasar Amurka Barack Obama da na Rasha Vladimir Putin, don tattauna matakan da za su dauka wajen yaki da kungiyar da'awar kafa daular musulunci ta IS.
Yayin da firaministan Valls ke zantawa da manema labaru a ranar 17 ga watan, ya ce, shugaban Hollande zai gana da Barack Obama a Washington, kuma zai gana da shugaban Putin a birnin Moscow, don kafa wani kawance na musamman wajen yaki da kungiyar IS.
Bugu da kari, kasashen Amurka, Australiya, da Belgium sun inganta harkokin tsaro bi da bi.(Bako)