in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
IS ta dauki alhakin kai harin kunar bakin wake a birnin Aden na kasar Yemen
2015-10-07 14:59:51 cri
Kungiyar IS mai fafutukar kafa daular Islam ta sanar da cewar, ita ce ta kai harin kunar bakin wake a kudancin birnin Aden dake kasar Yemen wanda ya yi sanadiyyar hallaka sojoin hadin gwiwa 15 da kasar Saudiyya ke jagoranta.

A wata sanarwa da kungiyar ta IS ta fitar a shafin ta na twitter, ta ce, ita ce ta tura 'yan kunar bakin wake 4 don kai hari a otel din da Firaiministan Yemen Khaled Bahah ke zaune tare da makarraban sa da kuma jami'an tawagar sojojin kasar Saudiyya wadanda ke aiki a karkashin rundunar hadin gwiwa ta hadaddiyar daular larabawa a birnin na Aden.

Wannan dai shi ne hari na farko da kungiyar IS ta kai kan jami'an gwamnatin Yemen da kuma sojin hadin gwiwar kasashen larabawa.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China