Ma'aikatar wadda ta bayyana hakan a jiya Litinin, ta ce sojojin ta za su ci gaba da kaddamar da hare-hare kan mayakan IS da ke kasar Iraqi, har zuwa watan Maris na shekarar 2017, bayan da a baya ta tsara kammala aikin a shekarar 2016 mai zuwa.
Ministan tsaron Birtaniya Micheal Fallon wanda ya ziyarci kasar Iraqi, ya ce sojojin saman kasar sa sun kai daruruwan hare-hare ta sama kan 'ya'yan kungiyar ta IS da ke Iraqi, a wani mataki na taimakawa gwamnatin kasar a yakin da take yi da ta'addanci. Ya ce Birtaniya za ta ci gaba da ba da tallafi ga sojojin Iraqi ta sama, da duk wani goyon da ya dace a fannin gine-gine, da aikin jinya a fannin soji.
Tun daga rabin karshen shekarar bara, Birtaniya ta fara tura dakarun soji kasar ta Iraqi domin aikin ba da horo. A kuma watan jiya gwamnatin Birtaniyar ta sanar da cewa, za ta ci gaba da tura jami'an soja 125 zuwa Iraqi, don taimakawa wajen aikin horaswa, da kara karfin dakarun kasar na yaki da dakarun kungiyar IS.(Bako)