in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An harbe wani shugaban kungiyar IS
2015-08-22 13:42:28 cri
Kwamitin tsaron kasa ta Amurka ya bayyana a ran Jumma'a 21 ga wata cewa, shugaba mai matsayin biyu na kungiyar IS Fadhil Ahmad al Hayali ya rasu sakamakon harin sama da sojojin saman kasar Amurka suka kai a ran Talata 18 ga wata, kuma ana tsamanin cewa, rasuwar Hayali za ta kasance wata babbar koma baya ga kungiyar IS sabo da muhimmin matsayinsa cikin ayyukan dake shafar kudi, soja, kafofin watsa labarai da kuma sufuri na kungiyar IS.

A wannan rana kuma, brigadier janar na rundunar sojojin ruwa ta kasar Amurka Kevin Killea ya bayyana a yayin taron maneman labarai cewa, bisa binciken da sojojin kasar Amurka suka yi game da boma-bomai da dakarun kungiyar IS suka yi amfani da su a yayin yakin da aka yi tsakanin kungiyar IS da kungiyar Kurdish a arewacin garin kasar Iraq, an tabbatar da cewa, boma-boman da kungiyar IS ta yi amfani da su suna da kayayyaki masu guba. Sai dai ya ce, a halin yanzu, ba za a iya tabbatar da cewa ko kungiyar tana amfani da makamai masu guba ba, sai bayan an gudanar da karin bincike kan makaman kungiyar. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China