Sanarwar ta ce, jiragen saman yaki na Faransa sun jefa boma-bomai 20 kan sasanonin kungiyar ISIS dake al-Raqqa na kasar Syria. Kungiyar na amfani da daya daga cikin sansanonin a matsayin cibiyar ba da umarni, inda ake daukar sabbin 'yan kungiyar, da ajiye makamai da albarusai. Yayin da take amfani da sansani na biyun wajen horas da dakarun ta.
Sojojin Faransa sun yi amfani da jiragen saman yaki 12 wajen kai wadannan hare-hare, ciki har da jiragen yaki masu dauke da boma-bomai guda 10, jiragen saman da suka tashi daga hadadiyyar daular Larabawa gami da kasar Jordan. Kafin gudanar da aikin, sai da aka sanar wa sojojin Amurka irin matakan da za a dauka. (Bello Wang)