Mista Zhang a lokacin ganawar ya isar da kyakkyawar fata daga shugaban kasar Sin Xi Jinping zuwa sabon shugaba John Magufuli, inda ya ce Sin na dora babban muhimmanci kan dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. Haka kuma Sin tana fatan zurfafa hadin gwiwa da Tanzaniya a dukkanin fannoni da kuma kawo moriyar juna da samun bunkasuwa tare, sannan kuma Sin na gayyatar Shugaba John Magufuli da ya halarci taron koli na dandalin tattaunawar hadin kai tsakanin Sin da Afrika da za a kira a farkon watan Disamba a birnin Johannersburg na kasar Afrika ta Kudu.
A nasa bangare kuwa, Mista John Magufuli ya nuna godiya ga zuwan Mista Zhang a bikin rantsar da shi, kuma ya isar da gaisuwarsa ga shugaba Xi Jinping ta bakin Mista Zhang, inda ya yi fatan dukufa kan raya dangantaka tsakanin kasashen biyu a wa'adinsa. Mr. Magafuli har ila yau ya bayyana fatan kara yin hadin gwiwa da Sin don kai dangantakar dake tsakanin kasashen biyu zuwa wani sabon matsayi. Ban da wannan kuma, Mista John Magufuli yana nuna kyakkyawar fata na samun ci gaba mai armashi a taron koli da za a yi a Afrika ta Kudu. (Amina)