in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi bikin baje-kolin kayayyakin Sin a kasashen Afrika karo na 2 a kasar Tanzaniya
2013-09-11 16:10:10 cri

An kaddamar da bikin baje-kolin kayayyakin kasar Sin a kasashen Afrika karo na 2 a birni mafi girma na kasar Tanzaniya wato Dar es Salaam.

Taron wanda aka gudanar ranar 10 ga watan nan, na karkashin kulawar ma'aikatar harkokin kasuwanci ta Sin, an bude shaguna 265 a gun bikin baje kolin wadanda jimlar fadinsu ya kai muraba'in mita 5000.

Masana'antu kimanin 200 da suka fito daga larduna, da birane 14 na kasar Sin ne suka halarci taron, cikinsu, har da wasu shahararrun kamfanonin Sin 10, da suke cikin jerin sahun gaba na manyan kamfanoni 500 a duniya.

A jawabinsa na fatan alheri ga mahalarta bikin, firaministan kasar Tanzaniya Mizengo Kayanza Peter Pinda, ya bayyana cewa, wannan biki zai kara fahimtar da al'ummar Afrika yanayin irin kayayyakin da ake kerawa a kasar Sin, ya kuma bude kasuwarsu a sauran kasashe. A cewarsa hakan zai sa kaimi ga hada-hadar fitar da kayayyaki kasar zuwa kasashen Afrika.

A sa'i daya kuma, Pinda yana fatan masana'antun kasar Sin da kasashen Afrika, za su kara fahimtar juna da inganta hadin gwiwa, musamman ma ga masana'antun Afirka da suka dace su yi amfani da wannan dama, don shigar da fasahohin kasar Sin, da gaggauta kara fitar da kayayyaki masu tsada zuwa kasashen waje.

A nasa jawabi, jakadan Sin da ke kasar Tanzaniya Lv Youqing ya bayyana cewa, bikin zai kara kawo dama ga masana'antun kasar Sin wajen kara saka jari a kasashen Afrika.

Kididdiga ta nuna cewa, cikin 'yan shekarun nan, tattalin arzikin kasashen Afrika ya samu bunkasuwa sosai. A karkashin kulawa daga shugannin kasar Sin da na kasashen Afrika, an kara karfafa hakikanin hadin gwiwar dake tsakanin bangarorin Biyu, tare da raya harkokin cinikayyarsu cikin hanzari. A shekarar 2012, yawan kudaden cinikayyar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika ya kai dalar Amurka biliyann 198.49, adadin da ya karu da kashi 19.3 cikin 100 idan an kwatanta da na shekarar da ta gabata.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China