A wajen hadarin, direktan hukumar 'yan sandan yankin Dar es Salaam Suleiman Kova, ya sanar da cewa, mutane 36 sun mutu cikin wannan hadari, cikinsu har da wasu kananan yara. Kova ya ce, yanzu rundunar 'yan sanda ta fara tuhumar shugaban kamfanin gine-ginen ginin, da babban injiniya, da mai tantance ingancin ginin, da wasu mutane 6, inda bayan an tabbatar da kwarya-kwaryar sakamakon binciken, za a gabatar da wadanda ake zargi gaban kuliya.(Bako)