in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An soke sakamakon babban zabe a Zanzibar na kasar Tanzaniya
2015-10-29 09:56:37 cri
Hukumar zabe ta Zanzibar ta kasar Tanzaniya ta sanar a Laraban nan 28 ga wata cewa, an tabka magudi a yayin zaben shugaban kasa da zaben majalisar dokoki da aka shirya a ranar Lahadi 25 ga wata, don haka an soke sakamakon zabe.

A wannan rana, shugaban hukumar zabe ta Zanzibar Jecha Salum Jecha ta gidan rediyon Zanzibar ya sanar da cewa, sakamakon tabka magudi cikin zaben shugaban kasa da zaben majalisar dokoki, wato an keta dokar zabe da tsarin mulkin Zanzibar, shi ya sa aka soke sakamakon zaben, don haka za a sake shirya wani zaben. Ya kuma bukaci jama'a da su kai zuciya nesa, su jira karin bayani na nan gaba, amma bai bayyana lokacin da za a sake gudanar da zaben ba.

A wannan rana, hukumar zabe ta Tanzaniya ta bayyana cewa, soke sakamakon zabe a Zanzibar ba zai kawo tasiri game da babban zaben kasar Tanzaniya ba.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China