in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanin yada labarai na Star ya sami lambar yabo ta WQCS
2015-10-29 11:06:23 cri

Hukuma mai fadi a ji ta fuskar kimanta ingancin kamfanoni ta BID ta kira taro karo na 29 a birnin Paris na kasar Faransa domin sanar da jerin kamfanoni mafi inganci, inda kamfanin yada labarai na Star na kasar Sin dake Tanzaniya ya samu lambar zinariya a matsayinsa na kamfanin Sin daya kadai, yayin da sauran kamfanonin kasa da kasa da suka samu irin wannan lambar yabo sun hada da Walmart, bankin ING, TATA da dai sauransu.

An ba da labari cewa, an kafa wannan hukuma ne a shekarar 1975 wadda ta yi suna sosai a duniya, lambar yabo da take bayar a fannin ingancin kamfanoni ta zama tamkar lambar yabo ta Oscar ko Nobel ta fuskar cinikayya, wadda ke baiwa wasu fitattun kamfanoni a fannin karfin ba da jagoranci, kimiyya da fasahohi da karfin kirkire-kirkire da sauransu.

An kafa kamfanin yada labaru na Star dake kasar Tanzaniya a shekarar 2009, wanda kuma yana tafiyar da ayyukansa a wasu manyan birane 16 a kasar, kuma ke ba da hidima ga mutane sama da miliyan 1, hakan ya kasance kamfani mafi girma a fannin watsa shirye shiryen talabijin na digital a kasar ta Tanzaniya. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China