in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Tanzaniya ya gana da manzon musamman na kasar Sin
2014-01-13 10:08:27 cri

A ran 12 ga wata a fadar shugaba da ke yankin Zanzibar, shugaban kasar Tanzaniya Jakaya Kikwete ya gana da manzon musamman na shugaban Sin Xi Jinping, kuma ministan gine-ginen gidajen kwana da birane da kauyuka Mista Jiang Weixin.

Mista Jiang ya isar da sakon gaisuwa na shugaban Sin Xi Jinping zuwa ga Jakaya Kikwete, tare da tayar shi murnar cikon shekaru 50 da samun nasarar juyin juya hali a Zanzibar. Jiang Weixin ya ce, Sin da Tanzaniya suna da zumunci mai zurfi, Sin ta taimakawa Tanzaniya gwargwadon karfinta, Tanzaniya kuma ta nuna goyon baya ga Sin kan batutuwan da ke shafar babbar moriyar Sin. Shekara ta 2014 shekara ce ta cikon shekaru 50 da kafuwar dangantakar Sin da Tanzaniya, Sin tana son yin kokari tare da Tanzaniya, don daga dangantakar hadin kai da abokantaka zuwa wani sabon mataki.

Shugaban Tanzaniya Mista Jakaya Kikwete ya nuna godiya kan yadda shugaba Xi Jinping ya turo manzon musamman Jiang da ya halarci bikin taya murnar cikon shekaru 50 da samun nasarar juyin juya hali a Zanzibar. A ganinsa, Sin ta dade tana ba da taimako ga bunkasuwar tattalin arziki da zaman al'ummar Tanzaniya, bangarorin biyu kuma sun samu kyakkyawan sakamako a fannoni masu yawan gaske, yana fatan kasashen biyu za su cigaba da inganta hadin kansu a fannin tsara fasalin birane da dai sauransu, ta yadda za su kara samun nasarori.(Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China