A ran 15 ga wata bisa agogon Tanzaniya, wani jirgin ruwan kamfanin man fetur na kasar Sin, ya kammala aikin shimfida batutun mai a tekun kasar, bayan shafe watanni 4 yana gudanar da wannan aiki. Hakan dai ya karya matsayin koli da kamfanonin Amurka da Turai suke da shi a wannan fanni.
An kaddamar da wannan aiki ne dai a watan Agustan shekarar 2013, wanda hukumar batutuwa ta kamfanin man fetur na Sin ta dauki nauyin gudanarwa. Tsawon batutun kuwa ya kai kilomita 540, wanda kuma ya shafe kilomita 29 a cikin teku.
Kammala wannan aikin, zai sassauta halin da ake ciki na rashin makamashi a Tanzaniya, musamman a babban birni Dar es Salaam. (Danladi)