Shugaban kasar Tanzaniya Jakaya Kikwete ya gana da manzon musamman na shugaban kasar Sin Mista Xi Jinping, kuma mataimakin shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Mista Chen Changzhi.
Bayan Mista Chen ya isar da sakon Xi Jinping na taya murnar cikon shekaru 50 na kafuwar Jamhuriyar Tarayyar Tanzaniya. Kafin ya bayyana cewa, Sin tana son yin kokari tare da Tanzaniya, domin zurfafa hadin kai da abokantaka a fannoni daban daban a tsakaninsu.
Kikwete ya nuna godiya ga takwaransa na Sin Xi Jinping da ya turo manzon musamman Chen ya halarci bikin taya murnar cikon shekaru 50 na kafuwar kasar a madadinsa. Ya ce, kasar Sin babbar abokiyar Tanzaniya ce, inda kana Tanzaniya na daukar kasar Sin a matsayin wata muhimmiyar abokiyartar hadin gwiwa. (Danladi)