in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
John Magufuli ya yi rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban kasar Tanzaniya
2015-11-06 11:01:23 cri
Zababben shugaban kasar John Magufuli, ya yi rantsuwar kama aiki a matsayin sabon shugaban kasar Tanzaniya, a wani taro da ya gudana jiya a birnin Dar es Salaam fadar mulkin kasar.

Yayin bikin, Magufuli ya ce sabuwar gwamnatin kasar za ta dukufa kamun da na'in wajen ganin ta raya kasar, da kawo alheri ga jama'a. A sa'i daya kuma, ya yi kira ga 'yan siyasar kasar daga bangarorin daban daban, da su kawar da bambancin ra'ayi, tare da watsi da abubuwan da suka wuce, da nufin samun bunkasuwa yadda ya kamata.

Manzon musamman na shugaban kasar Sin, kuma mataimakin shugaban majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Zhang Ping ya halarci bikin. Kaza lika shugabanni da kusoshin gwamnatocin kasashen Afrika ta Kudu, da Zimbabwe, da Kenya, da Rwanda su ma sun halarci wannan biki.

A 'yan kwanakin baya ne hukumar zaben kasar Tanzaniya, ta sanar da cewa John Magufuli, dan takarar jam'iyyar CCM mai mulki a kasar ne ya lashe zaben da aka gudanar a ranar 25 ga watan Oktoba, wanda hakan ya sanya shi zama sabon shugaban kasar.

John Magufuli mai shekaru 56, fitaccen dan siyasa ne a kasar Tanzaniya, ya kuma taba rike mukaman ministan kula da yankunan kasa da gidajen kwana da zamantakewar al'umma, da ministan ma'aikatar kula da kiwon dabbobi da na su, kana da ministan kula da gine-gine na kasar. (Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China