in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta kammala aikin samar da tsaftataccen ruwan sha a Tanzaniya
2015-08-13 09:38:05 cri
Gwamnatin kasar Sin a ranar talatan nan ta mika aikin samar da tsaftataccen ruwan sha ga kasar Tanzaniya bayan da ta haka rijiyoyi 55 da ke yankunan karkarar kasar tun daga shekarar ta 2013.

Aikin zai samar ma dubban mazauna yankunan tsaftataccen ruwan sha inji jakadan kasar Sin a Tanzaniya Lu Youqing a cikin jawabin da ya gabatar lokacin mika wannan aiki a Maneromengo dake yankin bakin ruwa mai tazarar kilomita 100 daga babban birnin Dar es Salaam.

Bayan kammala aikin wanda kamfanin kasar Sin mai suna China Geo-engineering corporation ta yi, kusan mutane 30,000 zuwa 40,000 a wannan yankin ne ake sa ran zasu samu tsaftataccen ruwan sha in ji Jakada Lu.

Wannan tsaftataccen ruwan sha na daga cikin alkawarin da gwamnatin kasar Sin ta yi ma Tanzaniya a lokacin taron hadin kai na ministoci karo na 4 tsakanin Sin da Afrika.

Ministan albarkatun ruwa da noman rani Jumanne Maghembe ya yaba ma kasar Sin a kan wannan hobbasa na ganin ta inganta rayuwar al'ummar Tanzaniya. Yana mai cewa rijiyoyin za su taimaka matuka wajen rage wahalhalun samun tsaftataccen ruwan sha da ake fama da shi a yankuna biyun dake kasar wanda aka dade ana fuskanta.(Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China