Taken bikin a wannan karo shi ne "Waves and Visions of Hope", wanda za a shafe kwanaki 9 ana gudanarwa. Kuma ana fatan gabatar da fina-finai 99 daga daraktoci 65 na kasashe 35. A karshe rukunoni 5 na alkalan dake tantance fina-finan da suka yi fice za su fitar da fina-finai 22 domin ba su lambobin yabo.
Kungiyar dake jagorantar shirya bikin ta bayyana cewa, ban da gabatar da fina-finai 99 ga masu kallo, za kuma a kira taron kara wa juna sani game da fina-fina, da dandalin tattaunawa, da taron 'yan jarida da sauransu, tare da gudanar da ayyukan nuna fasahohi da kide-kide, a kokarin kafa wani dandalin mu'amala, da samun fasahohi ga wasu masu aiki cikin sassan fina-fina na kasa da kasa baki daya.