in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kusan kammala aikin gina gada mafi tsayi dake reto a gabashin Afrika
2015-08-06 11:09:51 cri
Gadar Kigamboni mai tsawon mita 680, mafi tsayi dake reto ta gabashin Afrika, za a kammala nan da watanni, in ji darektan dake kula da aikin dan kasar Sin.

Kamfanonin kasar Sin CRCEG da CRMBEG suke ginin wannan gadar dake ratsa ruwan teku da kuma ta hada Kurasini zuwa Kigamboni a yankin hedkwatar tattalin arzikin Tanzaniya, Dar es Salaam.

Idan kome na gudana yadda ya kamata, bangarorin gadar za'a kammala hada su a cikin watanni biyu, in ji Zhang Bangxu, darektan kasuwanci na wannan aiki, tare da kuma gina wata hanya mai tsawon kilomita 5.7 da ke hadewa da wannan gada.

Idan aka kammala, gadar Kigamboni za ta samar wa al'umma wani sabon zabi na yin tafiye tafiye tsakanin yankunan biyu da ruwan teku suka raba, in ji jami'in tare da kara bayyana cewa tare da tsarin biyan kudi wucewa na zamani irin Dubai, amfani da gadar zai dauki gajeren lokaci fiye da daukar jirgin ruwan Ferry.

A cewar mista Zhang, an yi amfani da sabbin kayayyaki da sabbin fasahohin wajen gina wannan gada.

An yi amfani da igiyar karfe mafi karfi da inganci a duniya, da aka yi gwajinsu a wani dakin bincike na Chicago, in ji Li Haihong, darektan tafiyar da ayyukan wannan aiki.

Aikin gina wannan gada ya lakume dalar Amurka miliyan 135, kuma za'a kammala shi a karshen wannan shekara. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China