in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta sa ido sosai kan tekunta
2015-11-03 20:02:27 cri

Wani jami'in kasar Amurka da ba ya so a ambaci sunansa ya ce, kasarsa na da aniyar gudanar da sintiri a tekun Nanhai a kalla sau biyu-biyu a ko wadannen watanni 3, matakin da Amurkan ke fatan ci gaba da gudnar da shi a ko wace shekara.

Game da wannan batu, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Madam Hua Chunying, ta bayyana a wani taron manema labaru da ya gudana a Talatar nan cewa, Sin za ta maida martani ga ko wane irin mataki, da ko wace kasa za ta dauka na takala, kuma za ta ci gaba da sa ido sosai kan sararin sama da tekunta.

Haka kuma, Sin ta ja hankalin kasar Amurka, da ta dakatar da yin maganganu marasa dalili, ta kuma yi watsi da matakan takala da take nufin dauka, wadanda za su kawo illa ga ikon mulki da moriyar kasar Sin. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China