A yayin ganawar tasu, Yang Jiechi ya ce, an samu sakamako mai gamsarwa a yayin jerin tarurrukan da aka shirya don tunawa da kafuwar M.D.D., matakin da zai haifar da muhimmin tasiri game da makomar M.D.D., da kyautata alakar kasa da kasa.
Taron M.D.D. karo na 70 na da hakkin gudanar da ayyuka don cimma burin da aka saka a gaba yayin tarurrukan kolin M.D.D. da aka yi a baya, kuma kasar Sin za ta ci gaba da nuna goyon baya game da taron M.D.D.
Yayin da Mista Wang Yi ke ganawa da Lykketoft, ya ce, Sin ta nuna cikakken goyon baya ga M.D.D., kuma za ta bi tunanin da shugaban Xi Jinping ya gabatar a yayin taron koli na baya, don ganin M.D.D. ta samu ci gaba, tare da bude sabon shafin inganta hadin gwiwa tsakanin sassan biyu.
A nasa bangare kuma, Lykketoft ya jinjinawa babbar gudummawar da Sin ta bayar a yayin tarurrukan koli na M.D.D., yana mai yabawa muhimmiyar rawar da Sin ke takawa game da batutuwan M.D.D. Ya kuma yi fatan inganta hadin gwiwa da kasar Sin a cikin wa'adinsa. (Bako)