Madam Merkel ta bayyana hakan ne a yammacin jiya, yayin da ta halarci taron kara-wa-juna-sani na kasa da kasa kan batun raya yankunan karkara karo na 160 da aka shirya a birnin Beijing.
A shekarar 1961 ne asusun Körber Stiftung na Jamus ya kirkiro taron tattauna hanyoyin raya yankunan karkara ta yadda za a inganta fahimtar juna a duniya. Cibiyar nazarin batutuwan kasa da kasa ta sashen kula da tuntubar kasashen waje na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin da asusun Körber Stiftung ne suka shirya taron bisa taken 'Yadda tsarin kasa da kasa ke canjawa a halin yanzu'.
Merkel ta ce, Sin tana kara taka muhimmiyar rawa don sauke nauyin da ke kanta a matsayita na babbar kasa. Game da batun sauyin yanayi kuwa, Sin ta zama kasa ta farko cikin kasashe masu saurin bunkasuwar tattalin arziki, wadda ke kokarin cika alkawarin da ta yi game da rage yawan hayaki mai gurbata muhalli.
Ta kuma ba da misali cewa, Sin ta taka muhimmiyar rawa game da batun nukiliyar Koriya ta Arewa, kuma ta kawo sassauci game da halin kunci a zirin Koriya, kana ta tura sojojin kiyaye zaman lafiya don yaki da 'yan fashin teku a yankunan dake kusurwar Afrika.
Madam Merkel ta ce, a matsayinta na babbar kasa ta fuskar cinikayya da zirga-zirgar ruwa, Sin ta fahimci muhimmancin samar da tsaro a yankuna na duniya, inda kasar Sin ta bayyana kudurinta na ba da agaji a fannin soji da yawansu ya kai dalar Amurka miliyan 100 ga kungiyar AU, ta ce, wannan ya dace da shawarar da kasashen Turai suka gabatar.(Bako)