Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Madam Hua Chunying wadda ta bayyana hakan a yau, ta ce, kasar Sin tana bukatar Japan ta waiwayi tarihi kana ta kalli irin ta'asar da ta aikata a baya, sannan ta kaucewa duk wani mataki na amfani da karfi domin ta samu amincewa daga makwabtanta da kuma sauran al'ummomin kasa da kasa.
A jiya ne ministan shari'a na kasar Japan Mitsuhide Iwaki da takwaransa na harkokin cikin gida da sadarwa Sanae Takaichi suka ziyarci wurin Ibadar da ake kallo a matsayin wurin da aka karrama mutanen da suka tafka danyen aiki a duniya, yayin da shi kuma Abe ya aiki da sakon addu'a a gabanin ziyarar tasu.
Kasashen Sin da Koriya ta Kudu sun yi allah-wadai da ziyarar da jami'an kasar ta Japan suka kai wurin Ibadar na Yasukuni.(Ibrahim)