Mataimakin shugaban bankin raya Afrika(ADB) Mista Rémy Rioux ya bayyana a yau Alhamis cewa, yanzu ana samun muhimman canje-canje a Afrika, don haka akwai bukatar taimako da hadin gwiwa da kasar Sin a fannin hada-hadar kudi da zuba jari, ta yadda nahiyar za ta cimma burinta.
Mista Rémy Rioux wanda ya bayyana hakan a taron dandalin kasashen da kasuwanninsu ke tasowa na shekarar 2015 da aka yi a birnin Beijing cewa, ko da yake Afrika na samun ci gaba a 'yan shekarun baya, har yanzu nahiyar tana fuskantar kalubaloli daban-daban, ciki hadda matsalar bunkasuwar tattalin arziki, karancin muhimman ababen more rayuwa, rashin isassun guraben aikin yi da sauransu. Don haka ya ce, ya kamata Afrika ta kara zuba jari a bangaren muhimman ababen more rayuwa, ko da yake ana fama da karacin kudade a wadannan fannoni. Ban da wannan kuma, bukatar da Afrika ke da ita a fannin zirga-zirga, makamashi, sadarwa da sauransu ta kara samar da zarafi mai kyau ga kasuwanni masu tasowa ciki hadda kasar Sin. (Amina)