Majalisar gudanarwar kasar Sin ce ta bayar da wannan takarda, inda ta bayyana karara cewar, za ta fitar da jerin sunayen sana'o'i da fannoni da ayyukan da za a haramta zuba jari a kansu a kasar Sin, inda ta bukaci gwamnatoci a matakai daban daban na kasar Sin da su kwararran dauki matakan aiwatar da shirin. Ban da wadannan sana'o'i da fannoni da ayyukan da gwamnatin ta haramta, za a iya gudanar da ayyukan kasuwanci kamar yadda doka ta tsara. Sannan kuma an kasa jerin sunaye gida 2, wato jerin sunayen sana'o'i da za a haramta dukkan 'yan kasuwa na gida da na waje su zuba jari a cikin su a kasar Sin, gami da jerin sunayen sana'o'i da za'a haramtawa 'yan kasuwa na ketare zuba jari a cikin su.(Bako)