Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta mayar da martani game da jirgin ruwan sojan Amurka da ya kutsa cikin mashigin tekun dake kusa da tsibiran Nansha
A yau ne kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang ya yi bayani game da yadda jirgin ruwan soja mai suna Larson na kasar Amurka ya kutsa cikin mashigin tekun dake dab da tsibiran Nansha na kasar Sin, inda ya ce, kutsa kan da jirgin ruwan kasar Amurka ya yi ya kawo barazana ga mulkin kai da tsaron kasar Sin, da tsaron ma'aikata da na'urorin dake tsibiran, kana ya haifar da illa ga yanayin zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin. Saboda haka kasar Sin ta nuna rashin jin dadi da kuma adawa da wannan kutse.
Lu Kang ya ce, a ranar Talata 27 ga wata ne, jirgin ruwan soja na Larson ya shiga mashigin tekun dake kusa da tsibiran Nansha ba tare da samun amincewa daga gwamnatin kasar Sin ba. Hukumomin da abin ya shafa na kasar Sin sun sa ido da kuma yin gargadi ga jirgin ruwan na Amurka.
Lu ya kara da cewa, ko da yaushe kasar Sin na girmama da kiyaye 'yancin kasashe daban daban na yin zirga-zirga a tekun Kudancin kasar da ketare sararin saman yankin bisa dokokin kasa da kasa, amma tana adawa da ko wace kasa dake da yunkurin kawo illa ga mulkin kai da ikon tsaron kasar Sin, bisa dalilinta na wai tana da 'yancin zirga-zirga. (Bilkisu)