Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Hua Chunying ta tabbatar da hakan a jumma'ar nan lokacin da take ganawa da manema labarai a birnin Beijing.
Tace kasar zata cigaba da shiga ayyukan kiyaye zaman lafiya na MDD, zata kuma cika alkawarin ta na bada gudunmuwar kudi kamar yadda kason ta ya kama a majalissar, zata biya duk abin da ya kama nauyin ta a ayyukan kiyaye zaman lafiyar na MDD sannan kuma ta bada gudunmuwar ta ga zaman lafiya da tsaro na duniya baki daya.
Kasar Sin ta zama kasa na biyu mafiya bada gudunmuwa a bisa kididdigar MDD.
A lokacin taron kiyaye zaman lafiya da aka yi a cibiyar MDD dake birnin New York a ranar 28 ga watan Satumba, shugaban kasar Sin Xi Jinping yace kasar sa zata jagoranci kafa sashin ayyukan kiyaye zaman lafiya na din din din kuma zata kafa sojojin kiyaye zaman lafiya na jiran ko ta kwana guda 8,000.