Daga yanzu ma'aurata a kasar Sin za su iya haifar 'ya'ya biyu, lamarin da ya kawo karshen dokar nan ta tsawon shekaru da dama da ta haramta wa ma'aurata haifar da fiye da guda.
An dauki wannan mataki ne a karshen taron jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin a yau Alhamis a nan birnin Beijing.
Wata sanarwar da aka fitar bayan zaman taro karo na 5, na kwamitin tsakiyar jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin(CPC) na 18 da aka fara tun a ranar Litinin, ta bayyana cewa, an dauki wannan mataki ne don daidaita ci gaban al'ummar tare da magance matsalar karancin matasa da kasar ke fuskanta.
Tun a karshen shekarun 1970 ne aka kaddamar da shirin tsara iyali a kasar, inda aka baiwa iyalai mazauana birane damar haifar da daya tilo, kana 'ya'ya biyu ga iyalan da ke yankunan karkara, idan har suka haifi 'ya mace. Daga bisani kuma an sassauta wannan doka, ta yadda iyalai za su iya haifar da na biyu, idan har dukkan iyalan su kadai ne a wajen iyayensu.
Bugu da kari, an sassauta wannan doka a watan Nuwamban shekarar 2013, bayan zaman taro na uku na kwamitin tsakiya na JKS na 18
Za a fara amfani da wannan doka ce da zarar ta samu amincewar majalisar kafa doka ta kasar, wato majalisar wakilan jama'ar kasar Sin.(Ibrahim)